
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya yi maganin duk wasu, waɗanda ya kira da munafukai, da ke son haddasa rikicin tsakanin da da mai gidan da, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Da ya ke jawabi a wajen bikin cikar Kwankwaso shekaru 69 da haihuwa z wanda ya gudana a gidan Kwankwasiyya na Miler Road a jihar Kano a yau Talata, gwamna Abba ya ce duk mai don ya ga ya rabu da Kwankwaso to sai dai ya ji kunya.
A cewar sa, Allah ne Ya baiwa al’umma Sanata Kwankwaso kuma duk mai kunshe shi to ba mai son ci gaban al’umma ba ne.
“Duk munafukai na gida da na waje da ke son su ga mun rabu da Kwankwaso to ku gaya musu karyar su ta sha ƙarya.
“Da Kwankwaso, da Abba da yan jam’iyya duk muna nan daram-dam. Allah kai mana maganin wadanda basa don zaman lafiyar mu, “