Za a yi babban taron ne a Abuja cikin watan Fabarairu duk da cece-ku-ce da zargin siyasa sakamako bayyanar allunna tallata taron Babban Birnin na Tarayya
Alamu na kara tabbatar cewa an shirya gudanar da babban taron Al’qurani na Najeriya, wanda aka yi wa lakabi da ‘Nigeria Quranic Conference.’
Hakan ya biyo bayan bayyanar wani allon talla a babban birnin tarayya Abuja, wanda ke dauke da bayanai kan taron.
Allon ya nuna cewa za a gudanar da taron a ranar 22 ga watan Fabarairu a filin wasa na Mashood Abiola dake Abuja.
Taken taron shi ne ‘Littafinmu daya, Imaninmu daya, Al’umma daya.’
Haka kuma an gano wata sanarwar gayyatar taron, wadda ta fito daga fadar Sarkin musulmi.
Tun bayan fitowar bayanai kan fara shirye shiryen gudanar da taron, al’umma da dama sun suna kin amincewarsu da zargin cewar na siyasa ne aka fake da addini.
Tun da fari, wani dan jarida dan Najeriya mazaunin kasar China ne ya fara fallasa cewa gwamnatin tarayya na taron.
Domin tara malaman addinin musulunci da makaranta Al’qur’ani a Abuja, don nunawa duniya cewa har yanzu gwamnatin Tinubu na ci gaba da samun goyon bayan ‘yan arewa, musamman malamai.
Kwanaki biyu bayan nan, aka ji shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau yana cewa zasu shirya taro na musamman na hadin kan malaman addinin musulunci da makaranta Al’qur’ani a kasar.
lamarin da ya janyo cece ku ce.