Sama da mutum 400 ne hare-haren Isra’ila suka kashe a Iran tun bayan ɓarkewar yaƙin a ranar 13 ga Yuni, kamar yadda kakakin ma’aikatar lafiya ta Iran ya bayyana.
Hossein Kermanpour, ya rubuta a shafinsa na X cewa mutum 3,056 ne suka jikkata.
Ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin, akwai mata 54, da ma’aikatan jinya 5, sannan ya ce mafi yawan waɗanda aka kashe ɗin, fararen hula ne.
Wannan ne karo na farko da aka fitar da ƙididdigar waɗanda aka kashe a hukumance tun daga ranar 15 ga Yuni lokacin da hukumomi suka sanar da cewa an kashe mutum 224, an jikkata 1,200.
Tun da farko, kamfanin dillancin labarai na Nour ya sanar da cewa aƙalla mutum 430 aka kashe, sannan aka jikkata 3,500 a Iran.
