
Ana zargina da laifukan cin hanjci da rashawa da kuma cin amanar kasa ta hanyar kashe mu raba, zargin da ya yi ta musanta wa.
An gurfanar da Mista Netanyahu ne a kotun kasar domin ya amsa tambayoyi a shari’ar da aka jima ana yi zarginsa da aikata manyan laifuka uku na cin hanci da rashawa da kuma cin amana.
Masu gabatar da kara na zargin shugaban da aikata laifukan da suka hada da karbar cin hanci da zamba da kuma cin amana na yafiyar harajin Dala miliyan 500 ga wani kamfanin sadarwa.
A inda kamfanin na Bezeq Telecom zai tallata shugaban da matarsa Sarah a wani shafin yada labarai na kamfani, karkashin wani shiri na cudeni-in cudeka ta bayan fagge.
A kan haka yake fuskantar zargin bayar da cin hanci da kuma cin amanar dukiyar al’umma da aka ba shi.
Sannan kuma ana zargin shi da matarsa da karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 21,000 daga wani furodusan finafinan Amurka ta Hollywood, dan kasar Isra’ila mai suna Arnon Milchan da kuma wani attajirin kasar Australiya James Packer.
Aminya ta rawaito cewa, Natanyahu na kuma fuskantar zargin kulla yarjejeniyar da mamallakin kamfanin jaridar ‘Yedioh Ahronoth’, Arnon Mozes, domin tallata shugaban.
Yayin da shi kuma zai yi dokar da za ta hana bunkasar wata jaridar dake gogayya da ita, a wani salo na da bayyana da rashawa ne.
Tun shekarar 2020 Netanyahu ke fuskantar wadannan zarge-zarge, amma ya musanta aikata ba daidai ba.