
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar tuntubar juna ta Arewa (ACF) ta karrama dalibar da ta ci gasar turanci ta duniya Amina Abdallahi Aminu da kyautar naira miliyan daya.
Kungiyar reshen Kano ta karrama dalibar a sakatariyar ta dake nan Kano ranar Lahadi.
Amina Abdallahi Aminu ‘yar asalin jihar Yobe Mai shekaru 17 ta yi nasara a gasar turanci ta duniya bayan da ta doke dalibai daga kasashe 69 a watan Agustan da yagabata.
Da yake jawabi shugaban kungiyar reshen Kano Dr. Gwani Farouk Umar, ya ce sun rubutawa bankin Zenith ya karrama dalibar da takwarorinta 3 da suka yi nasara daga Najeriya.
Ya ce bankin ya baiwa kowacce daga cikin wadanda suka yi nasara su uku kyautar naira miliyan 5.
Ya ce kungiyar tuntubar juna ta Arewa ta yabawa bankin bisa kyautar da yayi musu.
Dr. Gwani Farouk ya ce bisa yin zarra da Nafisa Abdallahi Aminu ta yi wacce mahaifiyatar ‘yar asalin jihar Kano kungiyar ta hannun shugabanta na kasa ta bata kyautar naira miliyan 1 da kyautuka daban daban.
A nasa bangaren shugaban kwamitin amintattu na ACF na kasa Bashir Muhammad Dalhatu, Wazirin Dutse, ya ce nasarar da daliban suka samu abin farin ciki ne ga Najeriya baki daya.
Ya ce wannan na nuna cewa idan aka baiwa ‘yan Najeriya dama za su yi fice a kowane mataki a duniya.
Bashir Dalhatu ya kara da cewa nasarar da suka samu abin koyi ne ga sauran dalibai da al’ummar Najeriya.
Itama dalibar da aka karrama Nafisa Abdallahi Aminu ta bayyana farin cikin tare da yin kira ga sauran dalibai su kara jajircewa.
Yayin taron ACF ta kuma karrama Farouk Muhd Gumel, bisa gudunmawar da yake bayarwa da kuma nada shi shugaban asusun bunkasa tattalin arziki da kasar Bostwana ta yi.