Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta janye yajin aikin gargadi na kwana uku da mambobinta suka shiga a Abuja.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. George Ebong ya fitar ranar Juma’a ya ce sun dakatar da yajin aikin ne bayan da ministan Abuja Nyesome Wike ya shiga tsakani, inda aka biya musu da dama daga cikin bukatunsu.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne kungiyar ta tsunduma yajin aikin, kan rashin biya musu wasu bukatu da suka hada da bashin albashi da kuma kudaden alawus-alawus da sauransu.
A sanarwar janye yajin aikin, Dr Ebong ya ce tuni wasu daga cikin likitocin suka fara samun kudaden bashin da suke bi na karin albashi da ba a biya su ba na wata shida.
Shugaban ya ce bayan da ministan ya sa baki a kan bukatun nasu har aka fara share musu hawaye, likitocin sun koma bakin aiki a yau Asabar 25 ga watan Janairu, 2025.