Kamal Umar Kurna
Gwamnatin Kano ta ce zata mayar da hankali wajen tallafawa rayuwar mata da kuma matasan, a shekarar 2026 ta hanyar koyar da su sana’o’in dogaro da kai da basu jari.
Gwaman Kano Abba Kabir Yusif shi ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jagorantar bikin yaye dalibai guda 2,260 wadanda suka koyi sana’o’i daban-daban a cibiyoyin koyar da sana’oi guda 26 mallakin gwamnatin Kano.
Yace cibiyoyin koyar da matasan Kano sana’o’in an samar da su ne tun a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sai dai kuma gwamnatocin da suka gabata suka yi watsi da wuraran har suka dai na aiki.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma raba kayan sana’a ga dukkanin matasan da suka samu horon tare da jaddada cewa hakan zai bawa matasan damar fara sana’arsu kai tsaye.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar, Matasan sun samu horo a fannin sana’o’in kiwon Kifi, kiwon Kaji, na;ura mai kwakwalwa da harkokin fasaha, shukar tsirrai, kiwon dabbobi, tuki, aikin jarida da sauransu
