Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci manyan shugabannin rundunonin tsaron kasar nan su koma Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin su jagoranci yaki da matsalar tsaro kai tsaye bayan hare-haren bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Umarnin na zuwa ne bayan wasu fashewar bama-bamai da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 20 tare da jikkata fiye da 100.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Shugaba Tinubu ya bayyana harin a matsayin yunkurin karshe na ‘yan ta’adda da suke cikin matsin lamba daga rundunonin tsaron Najeriya.
Ya ce: “Wadannan hare-hare na nuna irin yadda ‘yan ta’adda ke kokarin tayar da hankalin jama’a yayin da rundunoninmu ke ci gaba da matsa musu lamba.”
Shugaban ya kuma yabawa sojojin Najeriya kan yadda suka dakile wasu bangarori na harin, yana mai cewa gwamnati za ta kara karfafa matakan tsaro domin kawar da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a fadin kasar.
A cewarsa, tuni ya amince da samar da sabbin kayan aiki da karin tallafin ayyukan tsaro domin karfafa kokarin rundunonin tsaron kasar.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin bayar da agajin gaggawa da su tabbatar da cewa duk wadanda suka jikkata suna samun cikakkiyar kulawar lafiya.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na cewa ba za a bar ko wani bangare na Najeriya ya zama mafakar ‘yan ta’adda ba.
