
Mahajjata fiye da miliyan ɗaya da rabi na hawan Arfa yanzu haka, ibada mafi girma a cikin rukunan aikin hajji.
Tun a jiya Laraba ne alhazan ciki har da na Najeriya suka isa tantunansu a Mina domin fara aikin Hajjin.







A bana ana sa ran zafin rana a Arafar ya iya zarce maki 40 na ma’aunin yanayi. Wannan ta sa gwamnatin Saudiyya kira ga mahajjatan da su kasance a cikin tantunansu, don kaucewa tsananin zafin ranar.
Haka kuma ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta yi gargaɗi kan mahajjatan, da su gujewa hawa tsaunuka a yau din, saboda hakan na gajiyar da jiki, baya ga kuma haɗarin fuskantar tsananin zafin da ka iya sanadin rasa rayukan jama’a.
Za ku sauraron hudubar fassarar hudubar Arfat kai tsaye daga Primier Radio a wannan shafi