
A yau 5 ga watan Mayu 2025 tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya cika shekaru 15 da rasuwa.
Tsohon shugaban ya rasu ne a bayan doguwar jinya yana kan mulki. Ya kuma kasance daga cikin daidaikun zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da talakawan ke kewar su, saboda kyakkyawan kamun ludayin gwamnatinsa.
An haifi marigayin ne a ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951, a unguwar ‘Yar Adua a garin Katsina.
Mahaifinsa Malama Musa ‘Yar Adua tsohon minista ne a jamhuriya ta farko, wansa kuma Janar Shehu Musa ‘Yar Adua, daya daga cikin jiga-jigan gwamnatin mulkin sojin Najeriya ne a shekarun 1970.
Malam Umaru Musa ‘Yar Aduwa ya yi malamin makaranta kafin ya shiga harkar siyasa, abin da ya kai shi samun nasarar zama gwamnan Katsina tsakanin shekarar 1999 zuwa shekarar 2007.

A lokacin da shugaba Obasanjo ya kawo karshen wa’adin mulkinsa a shekarar 2007, ya goyi bayan Umar Musa Yar Adua daga cikin tarin ‘yan takarar da suka nemi tsayawa zabe a jam’iyyar PDP, abin da ya kai shi ga samu nasarar kayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Abubuwan da ba za a manta da shi ba
‘Yar Adua yi zarra a dabi’arsa ta bin doka inda ya zaman shugaban kasa na farko da ya bayyana kadarorinsa ga al’ummar kasa. Uwa uba ya ba da umarnin sakin kudaden Gwamnatin Jihar Legas da gwamnatin Obasanjo ta ki saki daga Asusun Gwamnatin Tarayya.
Haka kuma kokarinsa wajen magance matsalar rashin tsaro da fasa bututun mai a yankin Neja Delta, ya bullo da shirin afuwa da tallafi ga tubabbun tsagerun yankin da suka ajiye makamai, har ya samar da ma’aikatar Neja Delta domin bunkasa yankunan da ayyukan hakar danyen mai suka lalata.
A cikin shekaru kusan 3 mulkinsa ‘Yar Adua ya rage farashin man da ya gada daga gwamnatin Obasanjo. Ya kuma inganta bunkasa bangaren ilimi da kula da lafiya da samar da kayan more rayuwa.
‘Yar Adua ya kuma soke sayar da matatun man kasar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi tare da tinkarar matsalar karancin man fetur wanda ya gada daga gwamnatin da ta gabace shi.
Marigayi ‘Yar Adua ya kaddamar da aikin janyo teku daga kudancin Najeriya zuwa arewacin kasar domin ragewa ‘yan kasuwa wahalar da suke sha wajen daukar kayan su a tashoshin jiragen ruwan dake kudancin kasar.
Tsohon shuagaban ya yi ta fama da rashin lafiyar da ta hana shi gudanar da ayyukansa kamar yadda suka kamata, abin da ya kai ga rasuwarsa a rana mai kamar ta yau ta 5 ga watan Mayun shekarar 2010.

Rashin lafiyar da rasuwarsa
Tun kafin zamansa shugaban a ranar 29 ga watan Mayun 2007, an yi masa dashen koda, lamarin da ya zama abin ce-ce-kuce a lokacin mulkinsa. A watan Satumban 2009 ya tafi kasar Saudiyya domin duba lafiyarsa, daga bisani aka sanar cewa yana fama da ciwon zuciya.
Dadewarsa yana jinya a kasar wace ta tare ya mika mulki ga mataimakinsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa ba ta haifar da rudani inda watan Fabrairun 2010 Majalisar Dokokin Najeriya ta yi amfani da karfinta ta ayyana mataimakinsa, Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin Shugaban Kasa.
A ranar 24 ga watan Fabarairu aka dawo da shi gida, amma Mukaddashin Shugaban kasa ya ci gaba da jan ragamar gwamnati.
Bayan watanni biyu, a ranar 5 ha watan Mayu Allah Ya yi masa cikawa, wanda haka ya ba damar rantsar da Jonathan a matsayin shugaban kasa.
Duk da rashin lafiyar Shugaba Yar’Adua ya samu farin jini a wurin al’ummar Najeriya musamman saboda manufofin gwamnatinsa 7 na ‘7 point Agenda’, wadda ya mayar da hankali wajen inganta makamashi da wadata kasa da abinci da samar da arziki da inganta ilimi da tsaro da sufuri da kuma mallakar kasa.