
A yayin da ’yan ƙasar Kamaru ke fita rumfunan zaɓe a yau Lahadi domin kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa, shugaban ƙasar mafi tsufa a duniya Paul Biya na son al’ummar ƙasar su sake zaɓarsa domin yin sabon wa’adin shekara bakwai.
Mutum fiye da miliyan 8.2 ne suke da rajistar zaɓe a ƙasar Kamaru wacce take da yawan jama’a da ya wuce mutum miliyan 30.
Kuma batun tattalin arziki da rashin aikin yi da matsalar tsaro su ne suka fi mamaye yaƙin neman zaɓen.
Mista Biya na Jam’iyyar Cameroon People’s Democratic Movement (RDPC), wanda a bana yake da shekara 92, ya fara mulkin ƙasar ne tun shekarar 1982, kuma bana yana neman wa’adi na takwas ne a jere.
Idan shugaban ƙasar ya samu nasara a babban zaɓen na ranar Lahadi, zai ci gaba da kasancewa a kan mulki har zuwa lokacin da zai kusa cika shekara 100 a duniya.