Tsohon gwamnan kuma Sanata ya fadi hakan ne a lokacin da shugaba Tinubu ya ayyana soma da dokar a watan Yuli tun kafin majalisar ta zartar da ita.
Malam Ibrahim Shekarau ya yi watsi da sabon tsarin rabon haraji da ake shirin aiwatarwa a Najeriya tare da kiran a tsaya a sake duba kudurin dokar sosai.
Shekarau ya bayyana hakan ne wata sanarwa ta matsayin da shi da wata kungiya suka dauka kan batun a wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi.
Sanarwar wacce mai magana da yawunta, Dakta Ladan Salihu, ya sa hannu ya ta ce, ya kamata a fayyace yadda tsarin zai gudana don guje wa rudani.
Domin rashin fayyace cikakkiyar ma’anar tsarin rabon zai iya kara haifar da rashin daidaito a tsakanin yankuna.
Sanarwar ta ce, tsarin bayar da kashi 30 bisa 100 zai fi amfanar wasu yankuna kadai, musamman Jihar Legas, tare da cutar da Arewacin Najeriya.
Shekarau da abokansa a sanarawar ta yaba wa Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), bisa amincewarta da sabon tsarin raba kuin VAT da sauran haraji. Yayin da suka yi kiran da a tabbatar da adalci ta hanyar danganta rabon kudaden da ainihin ayyukan tattalin arziki.
Kungiyar ta kuma roki Kungiyar Gwamnonin Najeriya da Kwamitin Gyaran Haraji na Shugaban kasa da su yi gyare-gyaren da suka dace don tabbatar da adalci a tsakanin kowa a Najeriya.