
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bukaci Majalisar Dokoki da ta ƙarfafa dokokin hana sayen kuri’a ta hanyar haramta wa ‘yan siyasa zuwa rumfunan zaɓe da maƙudan kuɗi.
Daraktan hukumar Tanimu Muhammed ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da jami’an tsaro da kwamitin gyaran dokokin zaɓe a Abuja a ranar Alhamis.
Tanimu ya jaddada cewa matsalar sayen kuri’a na barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
“Dakile matsalar ya zama dole a sanya iyaka ga yawan kuɗin da mutum zai iya ɗauka zuwa rumfar zaɓe, inda ya bada shawarar kada ya wuce N50,000”. In ji shi.
Taron dai na ƙarƙashin haɗin gwiwar Majalisar Dokoki da Cibiyar Bayar da Shawara ta Siyasa da goyon bayan ƙasashen Ingila da Burtaniya, domin inganta tsaro da dokokin zaɓe.