
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya , Antonio Guterres, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan rahotannin da ke nuna cewa Falasɗinawa 30 sun mutu a kusa da wata cibiyar raba kayan agaji da Amurka ke tallafawa a Zirin Gaza.
Guterres ya bukaci a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Ya jaddada cewa, “fararen hula da ma’aikatan agaji na bukatar kariya, ba farmaki ba.”
Rahotanni daga Gaza sun nuna cewa wasu Falasɗinawa da dama sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga a yayin da suke kokarin karɓar tallafi a cibiyar da ke kudancin Gaza.
Jami’an jinya sun tabbatar da cewa an bai wa waɗanda suka jikkata kulawar gaggawa a cibiyoyin lafiya na yankin.
Sai dai Isra’ila da wasu daga cikin ƙungiyoyin agaji da ke aiki a yankin sun musanta faruwar lamarin da ake zargi.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce, babu wani harbi da dakarunta suka yi a wannan wuri a lokacin da ake zargin lamarin ya faru, yayin da wata kungiya da ke tallafa wa cibiyar agajin ta bayyana cewa ba ta da cikakken bayani da ke tabbatar da mutuwar mutane a yankin.
A ranar Litinin da ta gabata, hukumomin lafiya na Gaza sun kara da cewa wasu Falasɗinawa uku sun mutu a wani farmaki na daban, amma sojojin Isra’ila sun musanta hakan.
Wannan lamari na ci gaba da ƙara janyo cece-kuce daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama, musamman dangane da yadda ake gudanar da hare-haren soja a yankin da ke fama da rikicin jin kai.
Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran hukumomin agaji sun dade suna gargadin cewa matsin lamba kan fararen hula a Gaza na kara tsananta, yayin da galibin al’ummar yankin ke fama da yunwa, matsin lissafi da karancin kulawar lafiya.
Guterres ya yi kira da a mutunta doka ta kasa da kasa da kare fararen hula, musamman a lokutan rikici.
Ya ce, “Wannan lamari ya kara nuna bukatar gaggauta tsagaita wuta da kuma samar da damar kai agaji ba tare da wata matsala ba.”