Bayanai daga Iran na cewa aƙalla mutane 500, sun mutu a sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, a cewar ƙungiyoyin kare hakkin Ɗan Adam da ke sanya idanu kan yadda zanga-zangar ke tafiya.
Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da Amurka ke barazanar ƙaddamar da hari kan Iran, matuƙar ta gaza kawo ƙarshen wannan zanga-zanga cikin ruwan sanyi ba.
Sai dai ba tare da wani ɓata lokai ba Iran ta mayar da martani, inda ta gargaɗi Amurka da cewa matuƙar ta kai mata hari kan matsalolinta na cikin gida, tabbas zata kwashi kashinta a hannu.
Zanga-zangar wadda ta fara da adawa da tsadar rayuwa yanzu ta juye zuwa ta adawa da tsarin gwamnati da Iran ke tafiya a kai tun shekarar 1979.
Wannan itace zanga-zanga mafi girma da kasar ke fuskanta tun 2022, kuma mahukunta sun lashi takobin kawo ƙarshen zanga-zangar ko ta halin ƙaƙa.
Ƙididdiga ta nuna cewa mutane 490, cikinsu 48 jami’an tsaro ne, sai wasu mutum 10,600 da aka kama cikin makonni biyu da aka shafe ana wannan zanga-zanga.
