Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na shirin sa haraji kan dukiyar gado da mammaci ya bari kafin a raba
Farfesa Kabiru Isa ne ya bayyana haka a wata doguwar takarda ta makala da ya rubuta kan shirin da gwamnatin Tinubu ke shirin kakaba wa ‘yan kasa amma ta bayan gida.
Shehun malamin dake tsangayar koyar da Ilimi da Kididdigar Kudi a Jami’ar Bayero a Kano ya ce, wannan shiri na harajin na daya cikin kudurorin dokokin da aka kai gaban Majalisar Kasa don amince wa da su amma hankalin jama’a bai kai kansu ba.
Kudurin dokar harajin kan dukiyar gado ta tanadi biyan wani kaso na haraji ga gwamnati daga abin da mamaci ya bari kafin a rabata ga magada.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya samar da wannan doka a zamanin mulkinsa amma marigayi Jnanar Sani Abacha ya soke ta a zamanin mulkinsa.
A bisa hujjar cewa hakan ya sabawa addinin Musulunci da na Kiristanci da mabiyansu ke da yawa a Najeria