Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya kori kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan tare naɗa Dakta James Atung Kanyip a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Malam Ibraheem Musa ya fitar
Gwamna Uba Sani ya kuma sanar da kafa ma’aikatar jin ƙai, inda aka naɗa Barde Yunana Markus a matsayin kwamishinanta na farko
A cewar Gwamnan, naɗin wanda zai fara aiki nan take, na da nufin ƙarfafa tsaro da kuma inganta harkokin mulki a jihar.
Bugu da ƙari Gwamna Uba Sani ya naɗa Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin kwamishinan kuɗi.
An kuma naɗa Farida Abubakar Ahmed, a matsayin babbar darakta (Rediyo) a kamfanin yaɗa labarai na jihar Kaduna (KSMC), yayin da Barista Vitus Azuka Ewuzie ya kasance babban mai taimakawa na musamman kan harkokin shari’a.
Sauran muƙaman da aka naɗa sun haɗa da Victor Mathew Bobai a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin jama’a da Abdulmutallib Isah a matsayin babban mataimaki na musamman kan ayyuka na musamman.
Sai Abdulhaleem Ishaq Ringim a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin tattalin arziƙi.