Hukumar Kidaya ta kasa NPC tare da hadin gwiwa da Ma’aikatar Lafiya Da Walwalar Jama’a na ci gaba da bincike domin gano musababbin mutuwar kananan yara a Najeriya.
Kwamishinan hukumar NPC reshen Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labaraI a shalkwatar hukumar a nan Kano.
Dakta Aminu Tsanyawa ya ce an samu rashe-rashen yara ‘yan kasa da shekaru biyar da dama da kuma mutuwar mata masu ciki a yayin haihuwa ko bayan haihuwar a kasar nan.
Wanda hakan ya sa suka fara gudanar da bincike domin gano musababbin matsalar
Kwamishinan Hukumar Kidayan ya ce, sakamakon binciken zai taimaka daukar matakan kariya da kuma magance matsalara baki daya.
Shuagaban ya kuma nemi hadin kan al’uma da hukumomi da ‘yan jaridu domin cimma abin da ake bukata.
Wakilinmu Faisal Abdullahi Bila ya rawaito cewa Daraktan hukumar Kidaya na kasa reshen Kano Alhaji Balarabe Kabir ya shawarci masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen binciken domin samun kyakkyawar kulawa da kuma kawo gyara a fanninn lafiyar iyali.