Fa’idar halartar Shugaba Bola Tinubu taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a Brazil na talaka ne domin muradin gwamnatin shine samar da yadda ‘yan Najeriya sun fi karfin abin da a za su ci.
Hakan ya fito ne daga bakin daya daga cikin manya hadiman shugaban a bangaren yada labarai Abdulaziz Abdulaziz a hirarsu da waikilinmu a Abuja farkon a ranar Litinin
Abdulaziz ya ce yana daga cikin dalilin halartar taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na G20 a Brazil da Shugaba Tinubu ke yi, watau bunkasa harkar noma ta yadda ‘yan Najeriya za su iya samar da abincin da za su ci har ma su fitar da shi zuwa kasar waje.
Ya kuma ce irin wannan ziyarce-ziyarce da shugaban ke yi a kasashen ketare na haifar da sakamako mai kyau duba da yadda masu zuba jari ke shigowa kasar nan.
Sannan ya kuma ce shugaban ya tafi taron ne da kwararru da masu ruwa da tsaki a fanin noma.
Ranar Asabar ne Shugaban ya bar kasar nan don halartar taron na G20 a Brazil wanda aka yi masa bisa gayyata ta musamman da aka yi masa.
Taron na kwanaki biyu na shugabannin kasashe 19 ne da suka hada Arjentina da Australiya da Kanada da Germany da Indiya da Indonesia da Italy da Japan da Koriya da Mekziko da Saudiyya da Afrika ta Kudu da Turkiyya da Ingila da Amurka da kuma Brazila mai masokin baki.
Sai kuma Kungiyoyin Tarayyar Afrika AU da kuma Kungiyar Tarayyar Turai EU.