Manyan Yan Siyasar da suka halarci daurin auren yar Kwankwaso
Ahmad Hamisu Gwale
A ranar Asabar din nan, manyan ’yan siyasa a ciki da wajen Najeriya, sun yi cikar kwari a Kano domin halartar daurin auren ’yar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da dan fitaccen attajirin nan Dahiru Mangal.
An gudanar da daurin auren Fahad Dahiru Mangal, da Aisha Rabiu Musa Kwankwaso a fadar Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi || wanda yan siyasa da dama suka halarta.
Mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shettima da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na daga cikin mahalarta daurin auren.
Haka zalika tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai Tajudden Abbas, suna daga cikin manyan ’yan siyasar da suka halarci daurin auren da aka yi a birnin Dabo.
A gefe guda ma, Sheikh Bala Lau, shugaban kungiyar Izala na kasa da Sheikh Kabir Gombe Sakataren kungiyar suna daga cikin wadanda suka halarci daurin auren.
A yayin bikin an hangi fuskar gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, da Sakataren Gwamnatin jihar Nasarawa Barista Aliyu Muhd Ubandoma Wazirin Lafiya.
Daga cikin tsaffin gwamnonin da suka halarci bikin akwai Ahmed Makarfi na Jihar Kaduna da Abdulaziz Abubakar Yari na Zamfara da Isa Yuguda na Bauchi, da Adamu Aliero na Jihar Kebbi.
Sai kuma Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, Abdulfah Ahmad na Kwara, Lucky Igbinedion na Edo, Mahmud Shinkafi na Zamfara da Victor Attah na Jihar Akwa Ibom.
A gefe guda Ministan Tsaro Muhammad Badaru Abubakar, da Major Hamza Almustapha, da Sanata Abdul Ningi, Sanata Lado Danmarke, Datti Baba Ahmed, tsohon dan takarar shugaban kasa na jamiyyar LP duka suna daga cikin wadanda suk halarci daurin auren.
Daurin auren yar Sanata Kwankwaso da na yar gidan Alhaji Dahiru Mangal, ya tara yan siyasa a Kano da aka dau shekaru ba aga fuskokinsu a Kano ba.
Har wa yau, Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi || da Gwamna Abba Kabiru Yusuf su ne wadanda suka zama masu ma saukin baki a taron bikin da aka gudanar.
Ana kallon dai, daurin auren ya zama tamkar wani taron sake saduwa bayan shekaru tsakanin manyan ’yan siyasar Najeriya da ba a ga sun hadu waje daya ba.
Wasu kuma na kallon haduwar yan siyasar na da alaka da tunkarowar zaben shekarar 2027 da ke tafe.