
Yajin aikin ma’aikatan Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) ya jefa tsarin zirga-zirgar jiragen sama cikin rudani tare da tilasta soke tashi da saukar jirage a manyan filayen jiragen sama na Abuja da Lagos da kuma Kano.
Tun ranar Laraba ne ma’aikatan NIMET sun fara yajin aikin da ya haifar da tsaiko mai yawa a harkokin tafiye-tafiye na jiragen sama.
Yajin aikin ya samo asali ne daga zargin ma’aikatan da gwamnatin kasa ta kasa fara aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashi na Naira 70,000.
Wannan mataki ya haifar da jin haushin ma’aikatan wanda ke cikin matsala wajen biyan bukatun su.
A halin yanzu, tsaiko da tarin fasinjoji sun bayyana a filayen jiragen, inda da dama daga cikinsu ke cikin damuwa game da makomar tafiye-tafiye da ayyukan su.
Wasu daga cikin fasinjojin ba su san lokacin da za su sake samun sabuwar tafiya ba.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa an shirya kiran taro da ma’aikatan a yau Alhamis domin tattaunawa kan yadda za a magance wannan matsala.
A cewar ministan, wannan yajin aiki yana kawo cikas ga harkokin sufuri, musamman ma ga ayyukan NIMET, wanda ke da alhakin kula da yanayi don tabbatar da aminci a zirga-zirgar jiragen sama.
NIMET tana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da amincin tashi da saukar jiragen sama ta hanyar ba da rahotanni kan yanayin da zai iya shafar tafiye-tafiye.