
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga jami’an hulɗa da jama’a da su rungumi kirkire-kirkiren fasahar zamani wajen gudanar da aikinsu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin gabatar da jawabi a lokacin taron bitar jami’an hulɗa da jama’a na shekarar 2025, wanda aka shiryawa jami’an hulɗa da jama’a daga dukkanin rassan Hukumar yaki da fasa kauri ta Ƙasa, wanda aka gudanar a Jami’ar Bayero dake nan jihar Kano.
Gwamnan, wanda babban daraktan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar Kano ta kulla kyakkyawar alaka da jami’an hulɗa da jama’a domin samun nasara wajen isar bayanan ga al’uma.
Ya jaddada muhimmancin aikin kafafen yaɗa labarai wajen isar da sahihan bayanai, inda ya ƙara da cewa wannan horo yana nuna yadda Hukumar yaki da fasa kauri ta kasa ta fahimci irin rawar da jami’an yada labarai suke takawa wajen tabbatar da bin doka da oda.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga jami’an hulɗa da jama’a daga dukkan ma’aikatu da hukumomi domin su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da kwarewa.
Wannan taro na ɗaya daga cikin manyan matakan da Hukumar Kwastam ke ɗauka don sauya fasalin aikinta tare da ƙarfafa dangantaka da masu ruwa da tsaki ta hanyar ingantaccen tsarin hulɗa da jama’a da dabarun sadarwa na zamani.
Taken taron shine: “Bayan kasancewa mai gabatar da taro: rawar da jami’an hulɗa da jama’a suke takawa wajen tabbatar da gaskiya da amana tsakanin su da masu ruwa da tsaki.”