
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya mika takardun neman izinin gina tashar jiragen ruwa mafi girma da zurfi a fadin Najeriya a jihar Ogun.
Da yake tattaunawa da jaridar Bloomberg ta Birtaniya, Alhaji Dangote ya ce tuni ya aike da bukatarsa ta yin haka domin fara aiki a gabar ruwa ta Olokola da ke jihar ta Ogun.
Attajirin ya kuma ce, gina tashar zai taimaka wajen saukaka fitar da kayayyaki waje daga Najeriya, daga ciki har da makamashin gas da kuma bunkasa rukunin masana’antunsa
.
