Ɗaliban Jami’ar Northwest da ke Kano sun gudanar da zanga-zanga biyo bayan ƙarin kuɗin makaranta da ya kai kashi 2,200%, inda aka kara kuɗin daga ₦19,700 zuwa ₦457,300 a sabuwar shekarar karatu ta 2024/2025.
Wannan ƙarin ya haifar da fargaba a tsakanin ɗalibai da iyayensu musamman a yanayin matsin tattalin arziƙin da Nijeriya ke ciki.
Ƙungiyar Ɗalibai ta Jami’ar (SUG), a cikin wata sanarwa da shugaban ta, Abdussalam Mahmoud Ahmad, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ta fahimci nauyin da ƙarin kuɗin ya ɗora wa ɗalibai. Ya ce “muna bibiyar duk wata hanya da za ta taimaka wajen neman mafita mai sauƙin da rage raɗaɗi,” duk da cewa ba su bayar da takamaiman lokacin da za a warware lamarin ba.
Wannan ƙarin kuɗin ya ƙara tayar da ƙura a tsakanin ɗalibai da iyayensu duba da yadda farashin karatu ke ci gaba da tashi a jami’o’i a faɗin ƙasar.
Ɗalibai da dama sun bayyana fushinsu a kafafen sada zumunta, musamman a X (Twitter), inda aka fara amfani da taken #NWUFeeProtest.
Izuwa yanzu, ba a ji wani bayani daga mahukuntan jami’ar ba dangane da dalilin wannan gagarumin ƙarin kuɗin lokac guda. Ƙungiyar Ɗalibai ta buƙaci a kwantar da hankali, tare da buƙatar dalibai su gabatar da ƙorafinsu kai tsaye zuwa ofisoshin ƙungiyar dake harabar Muhammadu Buhari Way Main Campus ko Ado Bayero House City Campus.
Wannan rikici ya ƙara bayyana yadda matsin tattalin arziƙi da rashin fayyace manufofi ke ci gaba da kawo cikas ga tsarin ilimi a Nijeriya, inda ɗalibai ke fama da ƙarin kuɗin makaranta da kuma ƙarancin tallafi daga hukumomi.
