
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi.
An kuma raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-Tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO) domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da faduwar darajar Naira sakamakon sauyin musayar kuɗaɗen waje.
Minista Edun ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja,
“Aƙalla gidaje miliyan 19.7 (sama da mutum miliyan 70) aka sanya a Rajistar Tsarin Tallafa Wa Talakawa. An kuma biyan tallafin ne ta hanyar aikawa da kudi kai tsaye ta asusun banki da kuma wayoyin hannu a, ta hanyar amfani da lambar NIN na kowane wanda zai ci gajiyar”. In ji shi.
Ministan ya kuma ce, za a ci gaba da saka shirin a cikin kasafin kuɗin shekara-shekara domin ya ɗore.
Shugabar NASSCO, Hajiya Funmi Olotu, ta bayyana cewa dalilin biyan tallafin kashi-kashi, shi ne saboda umarnin Shugaba na haɗa tsarin da lambar NIN, domin tabbatar da gaskiya.