Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, dake Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a.
A yayin bikin, Sakataren Gwamnatin, ya shawarci sabon Sarkin da ya ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.
Aminiya ta rawaito cewar, sabon Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed, ya gode wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan karamci.
Ya kuma yi alƙawarin yin biyayya ga Gwamnatin Jihar Bauchi da kuma Majalisar Masarautar Bauchi.
