Nadin sabon Babban Malami na madabo bayan rasuwar marigayi Alhaji Abubakar Kabiru ya bar baya da kura,
Dakta Suwidi Muhammad Hassan, Dan masanin Madabo, daya daga cikin wadanda suka nemi wannan matsayi dake jagorantar wani tsagi na gidan ya koka rashin adalci a lamarin.
A hirarsa da manema labarai a ranar Litinin, Suwidi ya ce, salon da aka bi wajen nada sabon babban malamin ya saba da al’adar gidan.
“Mu hudu ne muka kai takarda a rubuce ga ofishin wazirin Kano taa nuna sha’awar neman wannan matsayi da muka gada kaka da kakanni, amma masarautar Kano bata tuntube su ba, sai muka kawai muka ji a sama wai an zabi sabon Babban malami” in ji shi.
Dakta Suwidi ya kuma ce, kamata ya yi ace a fadar mai martaba sarkin Kano aka nada sabon Babban malamin kamar yadda ake wa masu unguwanni da dagatai, a matsayinsa na Sarkin Malaman Kano.
A makon jiya ne dai aka sanar da nadin Malam Abubakar Kabiru a matsayin babban malami na Madabo bayan rasuwar mahaifinsa.
