
Shugabannin ƙasashen Larabawa za su hallara a Riyadh babban birnin kasar Saudiya domin tattauna shirin sake gina Gaza da makomar yankin bayan yaƙin Isra’ila da Hamas.
Za su yi hakan ne bayan da kasashen suka yi watsi da matsayar Shugaba Trump na Amurka ta mallaki Gaza tare da kwashe Falasɗinawa daga yankin da kuma rarrabasu zuwa wasu ƙasashen Larabawa makwabta.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta gargadi cewa tilasta wa Falasɗinawa barin muhallansu ya saɓa wa dokokin duniya.
Taron zai kuma duba wanda zai ɗauki nauyin kuɗin sake gina Gaza da tsarin shugabancinta nan gaba.