Ranar Lahadi ne Alhazai daga fadin duniyai dake a birnin Makkah na kasar Saudiyya ke kammala aikin hajji, bayan kammala jifan shaiɗan a Jamarat da ke Mina.
Ko da yake a shari’ance a ranar Litinin ne ranakkun aikin Hajjin shida ke cika, saboda yadda addini ya bai wa mahajjatan damar kammalawa cikin kwanaki biyar ko shida inda kuma mafi yawan alhazan ke zaɓar kammalawa cikin kwana biyar ɗin.
Masu son ƙarawa su ma za su kammala ne ranar Litinin da jifan shaiɗan da ake kira Jamrat a rana ta huɗu maimakon uku da dama ke yi.
Gabanin jifan Jamarat ɗin, mahajjatan sun yi hawan Arafa da kwanan Muzdalifah da Ɗawaful Ifadah da kuma Sa’ayi
Ana sa ran soma kwaso alhazan Najeriya a mako mai zuwa.
