Kamfanonin sadarwa a kasarnan sun fara aiwatar da karin harajin kashi 50 cikin 100, biyo bayan amincewar da Hukumar Sadarwa Ta Kasa ta yi na karin.
Sai dai ‘yan majalisar wakilai sun dakatar da shirin, saboda matsalar tattalin arziki da kasar nan ke ciki.
A ranar Talata ne Majalisar Wakilai ta umurci Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa da kuma Ministan Sadarwa da Kirkire-Kirkire da Tattalin Arziki Na Zamani da su dakatar da karin kudin.
La’akari da halin da ‘yan Najeriya suke cikin na matsi da hakan, baya ga hauhawar farashin kayayyaki da kuma cire tallafin man fetur.
Masana tattalin arziki sun bayyana karin a matsayin abun da zai kara jefa Yan kasar nan cikin halin matsi.
