
Rasha ta harba ɗaruruwan jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami a Kyiv, babban birnin Ukraine lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 4 tare da raunata mutane da dama.
Rundunar sojin Ukraine ta ce Rashar ta harba jirage marasa matuƙi kimanin guda 595 da kuma makamai masu linzami guda 48 a cikin dare, amma ta ce makaman tsaron sararin samaniyarta sun kakkaɓo 568 daga cikin jiragen.
Rahotanni sun ce wasu mazauna birnin sun arce zuwa tashoshin jiragen ƙasa domin su tsira da rayuwarsu, a yayin da Rasha ke cigaba da kai hare haren.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya ce Rasha ta kwashe sama da sa’o’i 12 tana kai waɗannan hare-haren, wadanda suka lalata asibitin kula da masu matsalar zuciya, kana ta wargaza masana’antu, da kuma gidajen fararen hula.
Ya sabanta kiraye-kirayen ga ƙasashen duniya da su dauki tsaurararon matakan daƙile kuɗaɗen shiga da Rasha ke amfani da su wajen gudanar da yaƙin