
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba Da Sakandare JAMB ta ce, ba za ta kara wa’adin yin rajistar jarrabawar ta shekarar 2025 ba bayan ranar 8 ga Maris.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ya raba wa manema labarai a Abuja.
Benjamin ya ce, wa’adin rajistar da ya fara ranar 3 ga Fabrairu zai kare ne a ranar 8 ga Maris, 2025.
Sanarwar ta yi kira ga duk wadanda ke son zana jarrabawar da su yi rajista cikin gaggawa dan hukumar ba za ta kara wa’adi ba.
Sanarwar ta kara da cewa zuwa yanzu, sama da mutum miliyan 1.5 ne suka yi nasarar yin rajistar, wadanda suka yi daidai da hasashen hukumar a shekarar 2025.
