Ƙungiyar Likitocin masu neman kwarewa a Najeriya (NARD) ta sanar da tsawaita wa’adin da ta baiwa Gwamnatin Tarayya da makonni huɗu domin warware matsalolin da ta ce sun shafi walwala da yanayin aikin mambobinta.
Ƙungiyar ta ce idan ba a magance buƙatunta ba kafin wa’adin ya ƙare, za ta iya shiga yajin aiki a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyar ta bai wa gwamnati a baya. NARD ta ce har yanzu akwai batutuwan da ba a warware ba, ciki har da biyan kuɗaɗen horar da likitoci na shekarar 2026, bashin wasu alawus-alawus da kuma jinkirin biyan albashi ga wasu likitoci masu horaswa.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da barazana ga wasu mambobinta a wasu asibitocin koyarwa, tare da kira ga hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakan kare ma’aikatan lafiya da inganta yanayin aikinsu.
Sai dai NARD ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya a cikin wa’adin makonni huɗun, kafin ta yanke hukunci kan mataki na gaba idan har ba a cimma matsaya ba.
