
Mataimakin Babban Kwamandan Hisba na Kano Dakta Mujahiddeen Aminuddeen Abubakar ya yi kira ga masu shagunan cacar zamani da ake yi ta shafukan sada zumunta da su kuka da kansu, domin kuwa hukumar ta sanya kafar wando guda dasu
Dakta Mujahiddeen ya ce, addinin musulunci ya haramta kowane irin nau’i na caca, hakazalika dokar kasar nan ma, ta haramta caca, don haka a cewar sa, hukumar ba za ta sanya idanu tana kallon wasu batagari na kokarin bude irin wadannan shaguna a jihar Kano
Wannan dai ya biyo bayan fara bullar shaguna cacar zamani mai amfani da internet musamman ma a fagen kwallon kafa a jihar Kano
Inda matasa kan je domin yankar lamba tare da kintacen sakamakon wasanin da za a buga