
A ranar 21 ga Afrilu, 2025, cibiyar jin ƙai da bayar da agajin gaggawa ta Sarki Salman (KSrelief) ta samu nasarar kammala aikin tiyata 28 a sashen na’urar kara sauti ga yaran dake fama da matsalar ji a kasar Kenya.
Tiyatar ta kasance ƙarƙashin shirin bayar da tallafi na Saudia.
Wata tawagar ƙwararru guda 20 daga fannin likitanci daban-daban ne suka gudanar da ita.
Baya ga tiyatar, an kuma yi aikin wayar da kan iyayen yara 28 kan yadda yaran ke magana.
Wannan ƙoƙari na nufin samar da na’urar kara jin magana ga yara dake da matsalar kunne daga Kenya da Somaliya, domin ƙara taimakawa wajen ci gaban kiwon lafiya a yankin.
Wannan shiri yana daga cikin ƙoƙarin KSrelief na ci gaba da inganta rayuwar yara da ke fama da matsalar ji, domin basu sabuwar damar sake mu’amala da jama’a da kuma neman ilmi.