
Najeriya ta rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniyar kasuwanci da Saudiyya
Kasar ta kulla yarjejeniyar ne da Wani kamfanin bunƙasa Kayayyakin Halal na ƙasar Saudiyya.

Yarjejeniyar za ta bai wa Najeriya damar shiga jerin ƙasashen duniya da za su ci ribar da ta kai kimanin dalar Amurka har tiriliyan 7.7 a kasuwar halal ta duniya.
Haɗin gwiwar zai tabbatar da Najeriya a cikin jagororin bunkasa tattalin arzikin halal, tare da samar da ayyukan yi, da kuma janyo hankalin masu saka hannayen jari daga ƙasashen waje.
Yarjejeniyar za ta sauƙaƙe hanyoyin saka jari, da musayar bayanai da ilmin fasaha, da bude damammakin hada-hadar kasuwanci a cikin mahimman sassan ciki da wajen Najeriya, gami da samar da abinci, da magunguna, da bunkasa kiwon dabbobi.
“Yarjejeniyar Allura ce cikin ruwa da Najeriya ta yi rabon tsintowa.
“Domin yanzu Najeriya ta shiga jerin ƙasashen duniya da za su bigi ƙirji wajen cin gajiyar kasuwancin da ‘yan ƙasar za su yi na’am da ita.” In ji Sanata Ibrahim Hasan Hadejia Mataimakin shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Wanda ya wakilci Mataimakin Shugaban Kasa a Bikin sa hannu a yarjejeniyar.