
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta sanar da tarwatsa wani bam mai ƙarfi da aka gano a bayan ofishin NTA, kusa da hanyar Potiskum a birnin Damaturu.
Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce, rundunar ƙwararrun jamiʼai a fagen kwance bama-bamai da nakiya ne suka gudanar da aikin tarwatsa Bam din da karfe 10 na safe a wani fili mai nisa daga hedikwatar ’yan sanda a kan hanyar Gashua a birnin Damaturu.
Rundunar ta ce, ana iya jin ƙarar fashewar a sassa daban-daban na Damaturu, amma babu hatsari ga lafiyar jama’a.
Sanarwar ta kuma ce, an gano bam din ne yayin sintiri, kuma ana zargin ’yan gwangwan ne suka sayo shi daga wuraren da rikicin Boko Haram ya shafa, ko kuma sun tono shi daga ƙasa ba tare da sanin hatsarinsa ba.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya bukaci al’umma su rika lura da duk wani ƙarfe ko abu da suka ga ba su gane ba, su kuma kai rahoto ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.