Majalisar wakilai ta kasa ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin da hukumar WAEC daga amfani da kwamfuta a jarrabawar fita daga sakanadire ta shekarar 2026.
Majalisar ta kuma gargaɗin za a iya samun dalibai da dama da za su yi rashin nasara a jarrabawar da ake shirin yi a shekara mai zuwa.
Sannan ta umurci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da WAEC da su dakatar da shirin fara CBT na 2026 nan take. kuma ba da umarnin cewa kwamitocinta masu dacewa su zauna da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da fasaha, su mika rahoto cikin makonni hudu don ba da jagoranci ga doka ta gaba.
Honorabul Kelechi Nworgu (PDP daga jihar Ribas) ne ya gabatar da kudirin gaggawa a Majalisar Wakilai ranar Alhamis, 13 ga Nuwamba, 2025.
Dan Majalisar ya bayyana cewa makarantun sakandare na kasar, musamman na yankunan karkara, ba su da kayan aikin da suka dace don sauyin zuwa tsarin CBT.
Kelechi ya buƙaci majalisar ta shiga tsakani kan abin da ya ce zai iya zama barazana ga fannin ilimi.
“Duk da dai ana amfani da kwamfuta a jarrabawar JAMB, halin da akasarin makarantun sakandire ke ciki a faɗin kasar ina ganin sauyawa zuwa amfani da kwamfuta a jarrabawar 2026 ya yi wuri”. In ji shi.
Dan majalisar ya bukaci Ma’aikatar Ilimi ta Kasa da Hukumar Shirya Jarrabawar ta WAEC su ɗage fara amfani da kwamfuta na tsawon shekaru uku.
Kafin nan, an ɗauki matakan da su ka dace tare da samar da kayayyakin aiki.
