An zabo su ne daga cikin dimbin masu sauraron tashar da suka yi fice a mu’amilla da ita ta wayar tarho.
Tashar ta gayyato mutanen ne don kawo ziyara da kuma ganawa ta musamman don kyautata alaka da kuma magance matsalar kiran waya da wasu ke kokawa da shi.
Ziyarar za kuma ta ba su damar ganin gidan da ma’aikatanta da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu. a cewar shugaban Sashen Gabatar da Shirye-shirye na tashar Shehu Usman Salihu.
Gidan radiyon za ta gana ne da mutane 25 daga cikin dimbin masu sauron tashar, musamman wadanda suka yi fice a cikin masu kira wayar tarho.
Za a yi ganawar ce a harabar gidan radiyon dake kan titin Race Course a ranar 25 ga wata