
Hukumar kula da ‘yan fansho ta ƙasa (PTAD) ta bayyana kudirinta na ci gaba da tsayawa tsayin daka domin ganin ana biyan ‘yan fansho haƙƙokinsu da zarar sun kammala aiki.
Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga ƙorafe-ƙorafen da suka shafi jinkiri wajen biyan haƙƙin ma’aikata a jihohi da dama.
Babbar Daraktar hukumar, Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan a lokacin taron haɗin gwiwa da ‘yan fansho daga sassa daban-daban na ƙasar, wanda aka gudanar a birnin Kano.
Taron ya mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin da ke addabar ‘yan fansho a fadin Najeriya.
A jawabin da aka gabatar a madadin gwamnatin jihar Kano, shugaban ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa, ya yaba da kokarin hukumar, sannan ya bayyana cewa gwamnatin Kano na kare walwalar tsoffin ma’aikata da biyan haƙƙinsu akan lokaci.
Wasu daga cikin manyan jami’an hukumar da suka halarci taron daga jihohin Najeriya sun gabatar da ƙarin bayani kan abubuwan da aka tattauna da kuma shirye-shiryen da ke tafe domin ƙara inganta tsarin fansho.
Wakilinmu ya rawaito cewa taron ya haɗa shugabannin ƙungiyoyin ‘yan fansho daga fadin ƙasa domin tattauna hanyoyin magance matsalolin biyan haƙƙin fansho.