
Matatar man fetur ta Dangote ta sanar cewa za ta fara rarraba man kai-tsaye zuwa tashoshi a duk faɗin Najeriya daga ranar Litinin, 15 ga Satumba.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin na fitar a shafinsa na X.
Kazalika, kamfanin ya rage farashin man fetur ga masu gidajen mai zuwa N820 kan lita ɗaya, inda gidajen man jihohin Legas da sauran jihohin yammacin Najeriya za su sayar da shi kan N841.
Sai kuma Abuja da Rivers da Delta da Edo da Kwara za su sayar kan N851, daga baya shirin zai karaɗe sauran jihohin ƙasar.
Kamfanin ya ce an yi wannan tsarin ne domin rage farashin rarraba man da kuma sauƙaƙa farashin a tashoshi, da kuma rage matsin tattalin arziki.
Haka nan, ana sa ran tsarin zai amfani ƙananan masana’antu sama da miliyan 42 ta hanyar rage farashin makamashi da inganta ribarsu.