
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas (PENGASSAN) ta cewa za ta ci gaba da yajin aiki bayan zaman tattaunawa da Kamfanin Matatar Ɗangote da aka yi a daren Litinin ba a cimma matsaya ba.
Gwamnatin Tarayya ce ta kira zaman sulhun, bayan ƙungiyar ta zargi kamfanin da kora da kuma sauya wa ma’aikatanta kusan mutum 800 aiki.
Shugabannin ƙungiyar sun ce sai an dawo da su ne kawai za su janye.
Taron, ya samu halarcin shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, da wakilan Kamfanin Ɗangote, da sakataren kungiyar TUC Nuhu Toro, da kuma wasu jami’an gwamnati. Zaman da Ministan Kwadago Maigari Dingyadi ya jagoranta tare da Ministan Kuɗi Wale Edun.
Kamfanin Ɗangote ya ce, dalilin sallamar ma’aikatan shi ne zargin zagon ƙasa dake yin illa ga harkokin gudanar da kamfanin, hujjar da ƙungiyar PENGASSAN ta musanta ƙwarai.
Ana sa ran ci gaba da zaman tattaunawar a ranar Talata da yamma ƙarƙashin jagorancin Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi, tare da Ministan Kuɗi, Wale Edun.