
Tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya jinjina wa ‘yan Najeriya da suka lashe kyautar kwallon kafa ta CAF 2024 .
Kwankwaso ya jinjina wa Ademola Lookman ne a bisa abin da ya kira gagarumar nasara a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

“Ina mai jinjina ga tauraronmu dan Najeriya Ademola Lookman a bisa nasarar da ya samu na zama gwarzan shekarar 2024 na Hukumar Kula Da Kawallon Kafa ta Afrika CAF.
“Hakika Lookman ya taka rawar gani a gasar da aka gudanar na cin kofin Nahiyaa Afrika AFCON kuma hazikin dan wasana ga kungiyarsa ta Atlanta.
“Wannan jerin nasara da Najeriya ta samu a rukunin maza bayan nasarar Osimhen a shekara da ta wuce ya nuna irin kwazon ‘yan kasar a fannin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a duk inda suke” Inji shi.
Madugun na kwankwasiya ya kuma jinjinawa Chiamaka Nnadozie da ta zama Gwarzuwa mai tsaron gida a rukunin mata a gasar ta CAF.