Gwamnatin Tarayya ta musanta bai wa kamfanin bogi kwangilar ƙarasa aikin titin Kano zuwa Abuja.
Karamin ministan Ayyuka na kasa Bello Muhammad Goronyo ya sanar da hakan a yayin hirarsa da kafar yada labarai ta DCL a ranar Laraba.
Ministan ya ce, Kamfanin da ake ikirarin sun ba kwangila ba su san shi ba, Ba haka bane sun sa shi, kuma sahihi ne. arashin suna aka samu.
“Kawai suna kamfanin ya zo daya da wani irinsa, don haka zance da ake yada wa ba shi da kanshin gaskiya.”
Goronyo ya jaddada cewa, kamfanin sai da suka duba cancantarsa sannan suka duba cancantar sa tukunna.
Ya kuma kara da cewa, sun yi alkawarin cewa ma’aikatar za ta tabbatar da cewa an kamala aikin cikin lokaci kuma mai inganci