
Kamfanin NNPC ya ce yana tattaunawa da matatar Dangote kan tsawaita yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a naira.
Sanarwar ta biyo bayan rahotanni da ke cewa NNPC ya dakatar da sayar da mai ga matatar Dangote a naira.
Kamfanin ya musanta rahotannin, yana mai cewa yarjejeniyar za ta ƙare ne a ƙarshen watan Maris.

Masana na cewa idan NNPC ya dakatar da sayar da mai a naira, hakan na iya haddasa hauhawar farashi.