Ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’kamatis Sunnah (JIBWIS) a karamar hukumar Kankiya, jihar Katsina, ta sanar da rufe Masallacin Juma’a da ke unguwar Layi wanda ya shafe kusan shekaru 40 ana amfani da shi, sakamakon ambaliyar ruwa.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Sheikh Khalil Kasim, inda ya bayyana cewa daga yanzu za a riƙa gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Ibn Taymiyya da ke Gurara, wanda a asali masallacin salloli biyar ne na kullum.
Ya ce, “Sakamakon ambaliyar da ta mamaye masallacin, ba za a ci gaba da yin salla a can ba har sai wani lokaci.”
Shugaban JIBWIS na yankin, Alhaji Umaru Bature, ya bayyana cewa sun yanke wannan hukunci ne bayan taro da babban limamin masallacin, Malam Tasiu Umar, da kuma shugaban kwamitin kula da masallacin, Malam Alkhamis Rabiu.
Ya bayyana cewa masallacin bene ne, wanda aka gina tun kimanin shekara ta 1985.
Bature ya ce masana sun bayar da shawarar a rufe masallacin saboda ambaliyar ta mamaye shi baki daya.
