
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa wasu jihohin ƙasar za su fuskanci tsananin zafin rana na tsawon kwanaki huɗu.
A cewar hukumar, za a samu ƙaruwar zafi sosai a waɗannan ranaku, wanda zai iya shafar jin daɗin rayuwar jama’a.
Jihohin da za su fuskanci wannan matsanancin zafi sun haɗa da Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa, da Benue.
Sauran sun haɗa da Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi, Cross River, da birnin tarayya Abuja.
Haka kuma, Taraba, Adamawa, Plateau, Kaduna, Zamfara, da Sokoto su ma na cikin jihohin da za su fuskanci yanayi mai tsanani.
Hukumar ta kuma bukaci mutane da su riƙa shan isasshen ruwa, amfani da fanka da na’urar sanyaya ɗaki, da kuma zama a wurare masu inuwa domin rage tasirin zafin.