
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haɗakar ‘yan siyasa da za ta iya kayar da Tinubu da jam’iyyarsa ta APC a zaɓen 2027.
Shekarau ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa Dakta Sule YauSuke ya fitar a ranar Asabar.
Tsohon Sanatan ya bayyana haɗakar da wasu fitattun ‘yan siyasa suka yi da cewa wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa. Sai dai da sauran rina a a kaba.
“Babu daya daga cikin manyan jagororin da ke tafe da shugabancin jam’iyyarsa. Kuma taron wasu gungun mutane, duk da suna da manyan sunaye, ba za a kira shi ‘merger’ ba, domin a bisa doka, sai jam’iyyun da aka rijista ne kawai za su iya yin cikakken haɗaka.” In ji shi.
Furucin na malam Shekarau na zuwa ne bayan da Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Lebo Peter Obi, suka bayyana kudurin kalubalantar Tinubu da kuma shan alwashi kayar da shi a zaben 2027.