Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce ya kuduri aniyar shiga gaba cikin yunƙurin kawar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027, ta hanyar doka da dimokiradiyya.
Tambuwal, wanda shi ma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ne, ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Channels Tv, inda ya ce burin nasu shi ne ganin Najeriya ta samu sabon salo na shugabanci.
Kuma da taimakon Allah da al’ummar Najeriya, za mu samu nasara Wannan yunƙuri ba na Arewa kaɗai ba ne, yunƙuri ne na ƙasa baki ɗaya.
Sanatan ya yi watsi da maganganun da ake cewa haɗin gwiwar jam’iyyar ADC da sauran ƙungiyoyin adawa yunƙuri ne da Arewa ke jagoranta.
Ya ƙara da cewa babu wani tabbacin cewa Tinubu zai ci gaba da zama a ofis bayan 2027.
Duk ƙoƙarin da ake yi na nuna cewa Bola Tinubu ba zai fadi zaɓe ba, maganganu ne marasa tushe Zai iya faduwa idan ’yan adawa suka haɗu wuri ɗaya, kuma mu muna aiki domin ganin hakan ya tabbata a amfanin ƙasar nan.
Tambuwal ya kuma yi hasashen cewa Tinubu ba zai iya samun ƙalubale ba idan manyan jiga-jigan adawa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan suka tsaya kan tsari guda.
A cewarsa Idan kowannensu ya fito dabam a takara, Tinubu zai fi samun sauƙin nasara Amma idan suka haɗu, al’amura za su sauya, tsarin zabe kuma zai ɗauki sabon salo.
Sai dai ya ƙi bayyana wanda zai fi so ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 daga cikin jiga-jigan adawar, inda ya ce zai fito da matsayinsa ne idan dukkaninsu sun bayyana niyyarsuta tsayawa takara.
