
Jam’iyyar Hadaka ta ADC ta ce, Shugaba Bola Tinubu ba zai koma wa’adi na biyu ba idan ya ƙare mulkinsa a shekarar 2027
Domin ‘yan Najeriya ba za su ƙara zaɓensa don yin wa’adi na biyu ba.
Jam’iyyar na mayar da martani ne kan furucin Fadar Shugaban Ƙasa da ta ce Tinubu ba shi da niyyar ci gaba da mulki bayan shekarar 2031.
ADC ta kuma bayyana irin wannan magana a matsayin yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa kuma raina hankalin ‘yan ƙasa.
ADC ta zargi shugaban ƙasa da gazawa wanda hakan ya haddasa taɓarɓarewar tsaro da karuwar talauci da yunwa a ƙasar nan.
“Jama’a na fama da ta’addanci da kashe-kashe da tsadar abinci da haraje-haraje masu tsanani, yayin da gwamnati ta kasa kare rayuka da inganta rayuwar al’umma” in ji jam’iyyar.
“A maimakon shirin sake tsayawa takara, gwamnati kamata yay i ta mayar da hankali wajen amincewar jama’a don farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma rage raɗaɗin da talakawa ke fuskanta”.in ji Jam’iyyar
Sannan jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa a shekarar 2027, siyasa ba za ta kasance tsakanin APC da jam’iyyun adawa kawai ba, illa tsakanin jam’iyya mai mulki da al’ummar Najeriya baki ɗaya.